1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na ɗaukar ƙarin matakai na yaƙi da ta'addanci

Salissou BoukariNovember 22, 2014

Firaministan Faransa Manuel Valls da ke yin ziyara a wasu ƙasashen yankin Sahel ya jinjinawa dakarun ƙasarsa bisa ƙoƙarin da suke na yakar 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1DrhD
Frankreich Premierminister Manuel Valls
Hoto: Reuters

Firaministan ya ƙara jaddada aniyar ƙasarsa ta ƙara ƙaimi wajan ɗaukan matakai kan sabon salon ta'addanci da 'yan jihadi ke yi. Manuel Valls ya yi wannan furci ne a wannan Asabar ɗin a birnin Ndjamena na ƙasar Chadi, inda ya ziyarci rundunar sojan ƙasar ta Faransa wacce ake kira da sunan Barkhane da ke da aƙalla sojoji 1.300 a wannan ƙasa.

Da yake jawabi a gaban sojojin Firaministan ƙasar ta Faransa ya ce, ya na mai biye da su sau da kafa kan iri-irin aiyyukan da suka yi a 'yan makonnin baya-bayan nan, wanda hakkan ya sanya masu tadda ƙayar bayan suka gaza samun sukuni tare da rage musu karfi sossai.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane