Faransa: Sarkozy na komar 'yan sanda
March 21, 2018Watanni kalilan bayan hallaka Mu'ammar Gaddafi ne wata kafar watsa labarai mai suna Mediapart ta kwarmato cewar Nicolas Sarkozy ya samu tsabar kudi har miliyan 50 na Euro daga tsohon shugaban na Libiya domin gudanar da yakin neman zabensa a shekara ta 2007. Sai dai kuma tsohon shugaban na Faransa ya yi ta musanta wannan zargi ya na mai cewa ba shi da tushe balle makama. Sai dai Hukumar da ke yaki da cin hanci da karbar rashawa ta zurfafa bincike, inda ta saurari ba'asi daga shaidu da wadanda suke da hannu a wannan badakala.
Misali tsohon mataimakin hukumar leken asirin Libiyan Moussa Koussa ya bayyana cewar Mu'ammar Gaddafi ya taimaka wa Sarkozy da makudan kudade don ya gudanar da yakin neman zabensa. Haka shi ma wani dan kasuwa Ziad Takieddine ya ce tsohon shugaban Libiyan ya aiko shi da akwatuna uku na kudi domin bai wa Sarkosy da kuma na hannun damansa Claude Gueant a shekara ta 2007. Tuni dai mambobin jam'iyyarsa ta Les Républicains suka nunar da cewa kotu na yi wa Nicolas Sarkozy bita da kulli ne dangane da rawar da ya taka wajen kawar da Gaddafi a shekara ta 2011, inda ma 'yar majalisar dokokin Tarayyar Turai kuma tsohuwar ministan Sarkozy a yayin mulkinsa Nadine Morano ta ce Sarkozy ba shi da hannu a wannan laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Fadada bincike ga makusantan Sarkozy
Kotun Faransa da hukumar yaki da cin hanci sun fadada bincikensu zuwa ga na kusa da Sarkozy. Hasali ma dai tsohon ministan cikin gidansa Brice Horteufeux na daga cikin wadanda aka yi wa tambayoyi a ofishin 'yan sanda. Dama kuma an kama dan wani dan kasuwa mai suna Alexandre Djouhri sakamakon samunsa da hannu wajen kawo wani kaso na Kudi ga Nicolas Sarkozy da mukarrabansa. Sai dai Anne Genevard kusa a jam'iyyar Les Républicains tasu Sarkozy ta ce bita da kulli ake yi wa tsohon shugaban.
Tuni dai wasu ke danganta badakalar kudin da kuma matakin da Sarkozy ya dauka na afka wa Libiya da yaki tare da hallaka Muammar al-Gaddafi don hana gaskiya ta yi halinta. Siraji Issa shugaban kawancen kungiyoyin fararen hula na Afirka da ke fafutukar tabbatar da gaskiya kan kisan al-Gaddafi da al'umma a Libiya wato FISCA, na daga cikin masu wannan ra'ayi. Dama gamayyar ta FISCA ta shigar da karar Sarkozy gaban kotun duniya a bisa zargin aikata kashe fararen hula da kuma shugaban kasar Libiya Muammar Gaddafi.