1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Sarkozy ya sha kaye

November 21, 2016

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar adawa inda Francois Fillon ya zo na farko.

https://p.dw.com/p/2SzKY
Bildergalerie Paris Frankreich Autofreier Sonntag Autofrei
Hoto: Getty Images/AFP/D. Fage

Tsohon Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar adawa mai ra'ayin mazan jiya, yayin zagaye na farko na zabe, inda tsohon Firaminista Francois Fillon ya zo na farko amma ya gaza samun kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, domin haka zai kara zagaye na biyu nan da mako guda da Alain Juppe wanda shi ma ke zama tsohon firaminista, bisa shirye-shiryen zaben kasa baki daya na shekara mai zuwa ta 2017.

Yayin zaben Fillon ya samu fiye da kashi 44 cikin 100, kana Juppe ya tashi da kashi 28 cikin 100, lamarin da ya dakushe fatar Sarkozy ya zo na uku.

Shi dai Nicolas Sarkozy ya mulki kasra ta Faransa daga shekara ta 2007 zuwa 2012. Amma yanzu ya bayyana goyon baya ga Francois Fillon dan shekaru 62, wanda ya zo na farko.