1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ce Iran za ta iya taka muhimmiyar rawar gani wajen warware rikicin Gabas Ta Tsakiya.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoK

Ministan harkokin wajwen Faransa, Phillipe Douste-Blazy, wanda a halin yanzu yake kai ziyara a birnin Beirut, ya ce Iran na da muhimmiyar rawar da za ta iya takawa don samad da zaman lafiya a Lebanon da ma yankin Gabas Ta Tsakiya gaba ɗaya. Wannan jawabi dai, akasin matsayin da Amirka ta ɗauka ne, inda ita, take sukar Iran ɗin da ta da zaune tsaye a yankin gaba ɗaya, saboda goyon bayan da take bai wa kungiyar Hizbullahi. Ministan harkokin wajen Faransan dai ya nanata cewa, Faransa ba za ta yi zaman ’yamn ba ruwanmu ba, tana kallon yadda ake ta ragargaza ƙasar Lebanon. A cikin wata fira da ya yi da gidan talabijin ɗin FR2 na Faransan kai tsaye daga birnin Beirut, ministan ya bayyana cewa:-

„Ɗazu-ɗazun nan ne muka zartad da ƙuduri a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, wanda ya zayyana yadda za a tinkari wannan lamarin a huskar dipplomasiyya daidai, kamar yadda Faransa ta bukaci a yi: da farko shi ne tsagaita buɗe wuta ba da wani sharaɗi ba. Daga bisani ne kuma, za a cim ma yarjejeniya a siyasance, don share fagen girke dakarun ƙasa da ƙasa a yankin.“