1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ci Apple tarar kudi

Abdul-raheem Hassan
February 8, 2020

Hukumomin Faransa sun zargi kamfanin Apple da laifin rashin sanarwa mutane illar sabunta manhajar iOS na rage hanzarin tsoffin wayoyin apple.

https://p.dw.com/p/3XS6Q
New York City Apple Logo
Hoto: Reuters/M. Segar

Matakin ya zo ne shekaru biyu bayan da kamfanin apple ta yarda cewa sabbin manhajar iOS, ya rage hanzarin sauran wayoyin da aka kera shekarun baya.

A farkon watan Janairun 2018 wata cibiyar kare ingancin saya da sayarwa a Faransa, ta maka kamfanin kera wayoyin apple a kotu kan abinda ta kira zamba cikin aminci ta hanyar tirsasa mutane sayan tsoffin wayoyinsu ba tare da shedamusu illar ba.

Kamfanin apple ta amince da biyan tarar tare da yin na'am a kan matakin da zai ba ta damar inganta aikinta hulada da abokan cinikayyarsu.