1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta dakile yunkurin ta'addanci a lokacin Olympics

Abdullahi Tanko Bala
September 11, 2024

Daga cikin mutane biyar da aka kama, daya ya yi yunkurin kai hari kan cibiyoyin Yahudawa a Parisyayin da wani ya nufi daya daga cikin filayen wasan kwallon kafa.

https://p.dw.com/p/4kWck
Paris | 'Yan sandan Faransa a lokacin gasar Olympics
Paris | 'Yan sandan Faransa a lokacin gasar OlympicsHoto: Franck Fife/AFP

Hukumomin Faransa sun ce sun dakile yunkurin kai hare hare har sau uku a lokacin gasar wasannin Olympics na 2024 da aka kammala a birnin Paris. Babban mai gabatar da kara na Faransa ya sanar da haka.

Olivier Christen ya shaida wa gidan radiyon Farnceinfo a Faransa cewa an kama mutane biyar da ake zargi da yunkurin harin ta'addanci.

An kama mutanen ne cikin tsauraran matakan tsaro a lokacin da ake gudanar da wasannin

Hukumomin sun gudanar da samame gida gida har 936 ya zuwa yanzu a cikin wannan shekarar idan aka kwatanta da samame 153 da suka kai a bara.