Jigon IS a Mali ya shiga hannu
June 15, 2022Ma'aikatar tsaron Faransa ta ce an dauki tsawon makonni ana shirya wannan sumame a kusa da iyaka da Nijar, kafin a kama Oumeya Ould Albakaye. Kamen na zuwa ne a dai-dai lokacin da Faransa ke shirin kammala janye dakarunta daga Mali bayan da dakarun Barkhane suka shafe kusan shekaru 10 suna gwabza fada da mayakan jihadi a kasar.
Oumeya Ould Albakaye babban jigo a kungiyar IS a yankin Sahel, wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaye sunanta, ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa ana daukar Albakaye a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon Shugaban IS-GS Adnan Abu Walid al-Sahrawi, wanda sojojin Faransa suka kashe a watan Agustan 2021.
Albakaye kwararre ne a kan abubuwan fashewa, shi ne shugaban yankin kungiyar a yankunan Gourma a Mali da Oudalan a makwabciyar kasar Burkina Faso. Shi ne ma ke da alhakin yawan cin zarafi da ake yi wa fararen hula a wadannan kasashe biyu da ke fama da kalubalen tsaro.