SiyasaAfirka
Faransa ta musanta raunata farar hula a Burkina Faso
November 22, 2021Talla
Rahotanni sun ce sojojin na Faransa sun yi harbe-harbe a iska da harsashen roba don tarwatsa masu zanga-zangar. Sai dai daga bisani aka zarge su da harbin mutane da harsashi na gaskiya. To amma a wannan Litinin Pascal Lanni da ke magana da yawun sojojin na Faransa a Burkina Faso ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa bincikensu ya nuna sojojin ba su ji wa kowa rauni ba.
Mutanen Burkina Faso dai sun fusata ne da yadda suke zargin sojojin na Faransa da kasa tsare su a yayin da suke ci gaba da zama a kasar da sunan samar da tsaro.