Faransa ta yi sabon Firanminista
December 13, 2024Talla
Sabon Firanminista a Faransa, Francois Bayrou zai maye gurbin Michel Barnier, wanda ya aje mukaminsa a makon da ya gabata bayan da 'yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri'ar yankan kauna, lamarin ya sanya kasar cikin sabon rudani na siyasa. Faransa dai ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan zaben da aka gudanar a kasar a watanin Yuni da Yuli sun gaza samar da tabbatacen sakamako.
Karin bayani: Shugaban Faransa na shan matsin lamba kan sabon firaminista
Jam'iyyun adawa sun kuma bukaci Shugaba Macron ya yi murabus yayin da kasar ke kara fadawa cikin rudanin siyasa da na tattalin arziki, inda har yanzu ba a amince da kasafin kudin shekarar 2025, makwanni kalilan kafin a shiga sabuwar shekarar. Sai dai Shugaba Macron ya yi watsi da bukatunsu.