1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Macron ya zargi IS game da harin Rasha

Suleiman Babayo AH
March 25, 2024

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya jaddada batun cewa mayakan IS masu kaifin kishin addinin Islama ke da alhakin harin da ya faru a Rasha kuma duk yunkurin jawo Ukraine cikin lamarin ba zai haifar da alheri ba.

https://p.dw.com/p/4e6cl
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na FaransaHoto: Sebastien Nogier/AP/picture alliance

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce duk alamu sun nuna cewa tsagerun kungiyar IS suka kai hari a wajen kidar Gala a birnin Moscow fadar gwamnatin Rasha inda kusan mutane 140 suka halaka a kasrhen mako, kuma duk wani yunkurin mayar da lamarin kan kasar Ukraine ba zai haifar da alheri ga kasar ta Rasha ba. Shugaban na Faransa ya ce duk bayanan suke da shi na asiri sun nuna cewa mayakan IS suke da alhakin harin na Rasha.

Ita dai kasar ta Rasha tun farko ta yi watsi da batun Amirka da wasu kasashe cewa tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin Islama suka kai harin na karshen mako, maimakon haka kasar ta Rasha tana danganta lamarin da yakin da ke faruwa bayan kutsen da ta kaddamar kan kasar Ukraine. Tuni Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce akwai wasu daga bangaren Ukraine da suka shirya tabar maharan, abin da kuma mahukuntan Ukraine suka musanta.