1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta janye sojojinta daga Burkina Faso

November 21, 2022

Hukumomin Faransa sun ce babu mamakin za su kawar da sojojinsu da ke yaki da ta'addanci a Burkina Faso. Hakan na zuwa yayin da adawa da zaman sojojin ke karuwa a Afirka.

https://p.dw.com/p/4Joc2
Sojojin Faransa a yankin Sahel
Hoto: Daphné Benoit/AFP/Getty Images

Gwamnatin kasar Faransa ta ce ba ta fidda tsammanin janye dakarunta da ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Burkina Faso ba.

Zanga-zangar nuna kin jinin sojojin Faransa musamman a yammacin Afirka dai na ci gaba da karuwa a baya-bayan nan.

Ministan tsaron Faransar, Sebastien Lecornu ya ce gwamnatin kasar na da abubuwan nazari kan kasancewar dakarunta a kasashen Afirka.

Sai dai ministan ya ce sojojin kasar da ke sansanin Sabre na Ouagadougou babban birnin kasar ta Burkina Faso, sun taka rawa a yaki da mayakan tarzoma a yankin Sahel.

To sai dai ana ci gaba da turje wa zaman sojojin a kasar saboda shekaru da suka kwashe ba tare da kawo karshen mayaka masu ikirarin jihadi ba.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma dai sai da 'yan sanda suka tarwatsa daruruwan 'yan kasar Burkina Fason da suka mamaye ofishin jakadancin kasar da ke birnin na Ougadougou.