Ministan tsaron Faransa na ziyara a Ukraine
December 28, 2022Ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu ya isa birnin Kiev na kasar Ukraine a wannan Laraba domin tattauna hanyoyin ci gaba da taimakon kasar ta Ukraine wadda take fuskantar kutse daga sojojin Rasha. Ministan ya yi tafiyar daga kasar Poland mai makwabtaka da Ukraine, inda yake ganawa da manyan jami'an gwamnatin ta Ukraine.
Faransa tana sahun gaba kan taimakon da take bai wa Ukraine na kayan yaki na zamani da sojojin Ukraine suke amfani da su wajen kare kasarsu tun lokacin da Rasha ta kaddamar da kutsen ranar 24 ga watan Febrairun wannan shekara ta 2022.
A wannan Laraba an jira kara irin na gargadi gabanin hare-haren da Rasha ke kai wa, amma dai babu wasu sabbin hare-hare a sassan kasar ta Ukraine inda Rasha ke lalata kayayyakin more rayuwa na fararen hula.