1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa:'Yan sanda sun tsare Nicolas Sarkozy

Abdourahamane Hassane
March 20, 2018

Hukumar 'yan sanda mai yaki da cin hanci da karbar rashawa a Faransa ta tsare tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy tana yi masa tambayoyi a Nanterre da ke kusa da Paris saboda zargin cin hanci.

https://p.dw.com/p/2udTS
Nicolas Sarkozy
Hoto: Getty Images/AFP/G. van der Hasselt

Hukumar na binciken Nicolas Sarkozy ne a game  da zargin da ake yi masa na cewar tsohon shugaba kasar Libiya marigayi Muammar Gaddafi ya bashi kudade don yin kampe a zaben shugaban kasa na shekara ta 2007. Nicolas Sarkozy wanda ya yi mulki daga shekara ta 2007 zuwa 2012, wannan shi ne karo na farko da hukumar 'yan sandar da ke yaki da cin hanci take yi masa tambayoyi a kan wannan zargi.