1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula 16 sun mutu a yankin Darfur

Mouhamadou Awal Balarabe
July 22, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi bangarorin da ke rikici da juna da laifin cin zarafin bil'adama a Nyala da sauran sassa Darfur, inda rokoki ke salwantar da rayukan fararen hula da ke guje wa yakin Sudan.

https://p.dw.com/p/4UGJ5
Kashe-kashe na neman zama ruwan dare a yankin Darfur na SudanHoto: Scott Nelson/Getty Images

Akalla fararen hula 16 sun mutu a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, a lokacin da rokoki suka fada kan gidajensu sakamakon musayar wuta tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF. Dama dai Majalisar Dinkin Duniya na zargin bangarorin da ke rikici da juna da laifin cin zarafin bil'adama a Nyala da ke zama daya daga cikin wuraren da suka yi fama da yakin basasa a shekarun 2000.

Har yanzu dai, ana ci gaba da gwabza fada a Khartum babban birnin Sudan tare da yaduwa zuwa wasu sassa na kasar, watanni uku bayan fara yaki tsakanin shugaban gwamnatin mulkin soja al Burhan da mataimakinsa Hamdane Daglo. Amma ma'aikatan agaji na cin karo da cikas wajen gudanar da aikinsu sakamakon rashin samun izinin kutsawa lungu da sako na wuraren da ke fama da rikici.

Dubun dubatan 'yan Sudan da suka rasa matsugunansu na gudun hijira a kasashe makwabta, yayin da aka kasa samun alkaluma dangane da yawan mutane da suka rasa rayukansu a yakin na Sudan.