1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula 30 sun mutu a harin Siriya

Ramatu Garba Baba
September 10, 2017

A kasar Siriya an sami asarar rayuka da dama a sanadiyar hare-hare ta sama da jiragen yaki na Amurka da Rasha suka kaddamar a mabuyar mayakan IS da ke yankin Deir al-Zour.

https://p.dw.com/p/2jgSd
Syrien Kämpfe in Deir Essor
Hoto: Imago/Zuma Press

A rahoton da Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights ta fitar a wannan Lahadi ta ce fararen hula akalla 34 sun mutu a hare-haren sama cikin su har da yara kanana. Rayukan da suka salwanta inji sanarwar kungiyar wasu iyalai ne da ke kokarin fita daga inda ake barin wuta da sojojin kawance suka kaddamar kan mayakan kungiyar IS a yankin na Deir al-Zour mai albarkatun karkashin kasa, yankin ya fada hannun kungiyar a shekarar 2014 inda ta ci gaba da iko da birnin kafin wannan makon Amirka ta jagoranci farmakin fatatakar mayakan da ayyukansu ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane a kasar.

A daya bangaren kuwa Sojojin gwamnatin Siriya a wannan  Lahadi sun sanar da nasarar kwace da'ira ta karshe na zirin da ya hade gabashin birnin na Deir al Zor, da wannan nasara dai yanzu dukkanin hanyoyin sun dawo karkashin sojojin gwamnati a karon farko cikin shekaru.