Fararen hula a Ukraine na taimako a yaki
Watanni biyu da fara yakin Ukraine. Masana a fannin fasaha da sauransu na taimakawa wajen gina wuraren kariya da kuma kayayyakin kariya ga sojojin na Ukraine.
Kera silken kariya daga harin tankoki, a maimakon zanen taswira
Kafin yakin na Ukraine, Volodymyr Kolesnykov ya kirkiro masana'antar zanen taswirar karafa a Uzhhorod kusa da iyakar Hangari. Sai dai yanzu ya koma yin waldar silken kariya daga harin tankokin yaki.
Murhu domin dakarun da ke fagen daga
Yan Potrohosh tare da sauran masu fasaha, sun samar da murhun tafi da gidanka da za a iya amfani da shi a fagen daga da sauran wurare masu fama da tashin hankali a Ukraine. A nan yana nuna tambarin da suke mannawa a jikin murhun na tafi da gidanka da suke kerawa.
Daga dinkin jakunkuna zuwa rigunan kariya
Tun bayan barkewar yaki a watan Fabarairu, Sashko Horondi ya sauya salon sana'arsa. Maimakon dinkin jakunkunan na goyo, yanzu ya koma dinka rigunan kariyar harsashi ga sojojin Ukraine.
Gina badala a Odesa
Mazauna birnin Odesa da ke bakin teku, suna cike buhunhuna da yashi da ake amfani da su wajen gina badala domin kare birnin daga mamayar Rasha. Victor na daga cikin masu aikin sa-kai wajen bayar da tallafin ginin badalara, inda yake dauke da buhun yashin da ya dauko daga bakinn teku.
Koma mai launin kakin soja ga dakarun Ukraine
A birnin Ivano-Frankivsk da ke Kudu maso Yammacin Ukraine, masu aikin sa-kai sun taru a cikin wata Majami'a domin dinka komar sojoji mai laiunin kakin soja. A cikin wannan hoton, wata mace tana saka igiyoyi wuri guda domin tsara yadda komar sojojin mai launin kakin soja za ta kasance.
Yin saka tare
Jami'ar kimiyya da fasaha ta kasa da ke birnin Lviv, na zaman guda cikin cibiyoyin ilimi mafi dadewa da kuma aka fi martabawa a kasar Ukraine. A nan wasu mutane sun taru tare da hada hannu wajen saka komar mai launin kakin soja ga dakarun Ukraine, a lokacin da suke tsaka da yaki da makwabciyarsu Rasha.
This gallery was originally written in German