Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya
September 16, 2019Rahotannin da ke fito daga yankin takun Fasha na nuna cewa dakarun Iran sun kama jirgin ruwa dauke da kimanin kita-dubu 250 na man fetur da suke zargin na fasa kwabri ne daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan yana zuwa lokacin da farashin man fetur ya tashi a kasuwanin duniya bayan harin da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka dauki alhakin kai wa a kasar Saudiyya wanda ya kassara kimanin kashi 5 cikin 100 na man fetur da ake kai wa kasuwannin duniya. Tuni lamarin ya janyo tashin farashin man fetur da kashi 19 cikin 100, tashi mafi yawa da aka fuskanta a duniya tun skekarar 1991 lokacin yakin tekun Fasha na farko inda sojojin Iraki karkashin Marigayi Shugaba Saddam Hussein suka mamaye kasar Kuwait, sakamakon haka aka dauki matakan soja.
Yanzu haka fara ya kai Dalar Amirka 65.38, inda aka samu karin fiye da dalar fiyar kan kowacce gangar man fetur. Tun farko Amirka ta zargi Iran da hannu cikin farmakin na 'yan tawayen Houthi abin da mahukuntan Iran suka musanta. Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce gwamnatin kasar tana shirye da fitar da man fetur ka kasar ta tanada muddun lamura suka rincabe.