Ana neman makisan shugaban Haiti ruwa a jallo
July 8, 2021Talla
Tsananta binciken ya biyo bayan kashe wasu mutum hudu, tare da kama wasu biyu, 'yan sanda sun kuma ja kunnen duk wani mai hannu a kisan gillar da ya gaggauta mika kansa ga hukuma.
Kasashen duniya sun yi tir da kisan da ya jefa al'ummar kasar cikin rudani, yayin da masana harkokin tsaro ke fargabar makomar kasar da ta sha fama da tashe-tashen hankula a shekarun baya. Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na makonni biyu don nuna alhinin mutuwar Shugaba Moise mai shekaru 53.