Jamus na bukatar an tabbatar da dimukaradiyya a Sudan
February 28, 2020Kimanin jami'an gwamnatin da manyan 'yan kasuwan Jamus 70 ne dai suka yi wa shugaban na Jamus Frank-Walter Steinmeier rakiya a wannan ziyara ta kwanaki biyu da shugaban ke yi a Sudan, wanda shi ne shugaban kasa na farko da ya kai ziyara a Sudan din tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Omar Albashir. Shugaban na Jamus ya yi jinjina da irin nasarar juyin juya halin da aka yi a kasar, wacce ta kama hanyar dora kasar kan tafarkin dimukiradiyya na hakika, ya yi alkawarin taimaka wa kasar ta Sudan wajen mayar da ita cikin dangi da taimaka wa tattalin arzikinta: ''Duk da irin kalubalen da ke muke fuskanta, na yi ammanar cewa, bayan tattaunawar da na yi da shugabannin Sudan, za mu gudu mu tsira tare. Kuma cudeni in cudeka tsakaninmu kasashenmu biyu za ta kara inganta."
Ziyarar shugaban Jamus na cike da tarihi a cewar shugaban rikon kwarya na Sudan Abdel Fattah Abdelrahman Burhan
Shugaban hukumar rikwaon kwaryar na Sudan, Abdulfattah Burhan ya ce wannan ziyara tana cike da tarihi wacce za ta mayar da kasar Sudan cikin dangi a taikace, yana mai fatan Jamus din za ta jawo sauran kasashen Turai don kulla sabuwar alakar da Sudan: "Mun tattauna kan yadda Jamus za ta taimaka mana wajen ganin an cire sunan kasarmu daga jeri masu tallafa wa 'yan ta,adda. Da kuma yadda Jamus za ta taimaka mana wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a kasarmu, gami da tallafa mana don tinkarar babban kalubalen tattalin arzikin da muke fuskanta."
Shugaban na Jamus ya kuma gana da jagogrorin juyin juya halin, wadanda ya jinjina musu kan bajintar da suka nuna ,ya kuma sake karfafasu kan ba da hadin kai ga gwamnati rikwon kyarya domin ta samu ta tsallake siradi.