1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farfaɗo da hulɗa tsakanin Sabiya da tsoffin lardunanta

October 31, 2012

Hillary Clinton da Catherine Ashton sun yi kira ga shugabannin Kosovo da su matsa ƙaimi don samun ci-gaba a shawarwari da Sabiya.

https://p.dw.com/p/16a7N
Hoto: Reuters

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da babbar jami'ar kula da harkokin ƙetare na tarayyar Turai Catherine Ashton a wannan Laraba sun yi kira ga shugabannin Kosovo da su matsa ƙaimi don samun ci-gaba a tattaunawa da mahukuntan Sabiya. Manyan jami'an biyu sun kuma ce dole ne shugabannin na Kosovo su aiwatar da canje canje da za su kai ga ba su wakilici cikin tarayyar Turai da ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO. Bayan ganawarsu da firaministan Kosovo Hashim Thaci da shugabar ƙasa Atifete Jahjaga, an jiyo sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton na cewa babu gudu babu ja da baya a kan aiyana 'yancin kai da Kosovo ta yi wadda Sabiya ke matuƙar adawa da ita.

"Muna adawa da ko wace irin tattaunawa ta yi wa batun 'yancin kan Kosovo kwaskwarima ko sake buɗe wani babi na matsayin 'yancin kanta. Waɗannan ba batutuwa ne da za a sake tattaunawa kansu ba."

'Yancin kan Kosovo da ake taƙaddama kansa na zaman babban cikas ga hulɗoɗin dangantakun ƙasashen yankin Balkans. Clinton da Ashton dake rangadin yankin na Balkans na son Sabiya da tsoffin lardunanta su fara shawarwarin maido da dangantaku tsakaninsu. Ƙungiyar EU ce ke ɗaukar nauyin taron shawarwarin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas