1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Falasdinawa da Isra'ila yai

May 13, 2021

Rikicin ya barke ne tun a ranar Jumma'ar makon da ya gabata, lokacin da dakarun Isra'lan suka yi wa Falasdinawan da ke cikin Masallacin Al-aqsa da ke birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/3tMKD
Israel | Gaza | Konflikt
Isra'ila ta kai hare-hare Zirin Gaza, bayn harin rokokin Hamas na martaniHoto: Uncredited/AFP

Dama dai bangarorin biyu sun jima suna takun saka a tsakaninsu, domin rikicin Isra'ila da Falasdinu na zaman babban rikici da ke wakana a yankin Gabas ta Tsakiya. Isra'ila kan yi amfani da karfin tuwo na soja wajen kokarin murkushe Falasdinawan da mafi akasari kan yi amfani da duwatsu wajen yin fito na fito da dakarun na Isra'ila.

A hannu guda kuma, kungiyar Hamas da ke iko da yankin Zirin Gaza, kan yi amfani da rokoki wajen mayar da martani ga hare-haren sojojin na Isra'ila. Al'ummomin kasa da kasa dai kan nuna dan yatsa ga Isra'ilan, sakamkon yin kaka-gida a yankunan Falasdinawa. Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa, akwai fargabar wannan sabon rikicin, ka iya rikide wa zuwa yaki. Wannan fargaba dai ta sanya al'ummomin kasa da kasar yin kira ga bangarorin biyu da su mayar da wukakensu cikin kube.