1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Fargabar sabon nau'in corona a Birtaniya

December 21, 2020

Firaministan Birtaniya Boris Johnson na shirin jagorantar wani taro na gaggawa da kwararru kan barkewar sabon nau'i na coronavirus.

https://p.dw.com/p/3n17i
London Premierminister Boris Johnson
Hoto: Toby Melville/REUTERS

Sabon nau'in da acewar Firaministan Burtaniyar ke yaduwa fiye da kwayar cutar corona da akafi sani, yafi kamari ne a birnin London da kuma gabashin Ingila. Kawo yanzu lamarin ya tilasta wa sauran kasashen Turai rufe zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu da Birtaniya don gudun kar a kai  musu sabuwar cutar.  

Wasu daga cikin kasashen da suka dakatar da zirga-zirga a tsakinsu da Birtaniya sun hada da Rasha da Indiya da Kanada da Isara'ila da Saudiyya da Iran da kuma Moroko. Nan gaba a wannan Litinin ne wakilan kasashen Turai za su tattauna yadda za su tunkari sabon nau'in na corona.