1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar Rasha da kasashen duniya

February 21, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai tayi barazanar sanya wa Rasha takunkumi muddun ta kuskura ta aiyana yankunan 'yan awaren Ukraine a matsayin masu 'yancin cin gashin kai.

https://p.dw.com/p/47NnE
Bildkombo | Putin | Borrell | Biden
Hoto: Getty Images

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce, yana nazarin bukatar da 'yan awaren Gabashin Ukraine suka shigar, na son aiyana su a matsayin yankuna masu cin gashin kansu. Kungiyar Tarayyar Turai ta ce, za ta mayar da martani na sanya wa Rasha takunkumi muddun ta aiyana yankunan na Donetsk da Luhansk a matsayin masu cin gashin kansu.

Tun a makon da ya gabata ne, majalisar dokokin Rasha ta bukaci Shugaba Putin, da ya amince da yankuna biyu da Rashan ke mara wa baya a gabashin na Ukraine a matsayin kasashe masu cin gashin kansu. 

Majalisar ta ce, amincewa da yankin Donetsk da Luhansk, zai kasance muhimin mataki, wanda zai kawo karshen shirin zaman lafiya na Minsk a gabashin Ukraine, amma kasashen yamma sun baiyana shakku dama fargaba a zargin da suke ma Rashan na son mamaye Ukraine.