Salon karbe mulkin 'yan Taliban ya zama abin fargaba a Sahel
September 10, 2021Talla
A wata tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, M. Guterres, ya ce akwai mumunan hadari idan kungiyoyin suka koyi salon matakin karbe iko irin na 'yan Taliban, yana mai cewar dole ne a dauki kwakwaran matakai don kare yankin Sahel da ya kira mai cikakken rauni.
Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bukaci da a dage tarnakin da rundunar tsaro ta G5 sahel ke fuskanta don tallafa mata wajen tabbataar da tsaron yankin, yana mai cewa matsalar a yanzu ba wai ta tsaya a Mali ko Burkina Faso da Nijar kadai ba ne, a zahiri, ana ganin barazanar har zuwa wasu kasashen makwafta irinsu Ghana da Cote d'ivoire.