Fargabar Amurka da Israila kan makamashin nukiliyar Iran
March 5, 2012Shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Israila Banjamin Netanyahu zasu fara tattaunawa dangane da makashin nukilyar Iran a wannan litini, kasancewar kowane bangare na da niyyar bada nasa gudunmawa dangane da wannan batu da ya dade yana ci musu tuwo a kwarya.
A jawabin da yayi lokacin da ya halraci taron wata kungiyar da ke goyon bayan Israila, ya kushe duk wata magana ta kaddamar da yaki amma ya nuna amincewarsa da imanin da Israela ta yi, da cewa lallai Iran ta mallaki makaman kare dangi.
" babu gwamnatin Israilan da zata amince da kasancewar makaman kare dangi a hanun gwamnatin da ta karyata afkuwar kisan kiyashin da aka yi wa yahudawa, wacce kuma ke barazanar shafe Israila daga duniya tana kuma tallafawa kungiyoyin ta'addanci da ke barazana ga Israila"
Wannan cacar baki na makamashin nukiliyar ya tura tattaunawar sulhu tsakanin Israila da Falasdinu a kujerar baya to amma ana sa ran cewa shugabanin biyu zasu tattauna wannan batu.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal