1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zabe a Tanzaniya

Zainab Mohammed Abubakar
October 28, 2020

Tanzaniya na zaben da 'yan adawa ke fargabar za a yi magudi, bayan abun da suka kira shekaru na rayuwar kunci a karkashin mulkin kama karya na shugaba John Magufuli.

https://p.dw.com/p/3kWjw
Bildkombo Tansania Wahlen | Präsident John Magufuli und Tundu Lissu

A yankin Zanzibar mai kwarya kwaryar 'yancin kai, daruruwan maza da mata ne suka yi jerin gwano a layuka daban daban a garin Garagara, yankin da a jiya Talata 'yan sanda suka yi arangama da mutane da ya kai ga dukan fararen hula.

Shugaban adawar Tanzaniyar Tundu Lissu dai ya tsallake rijiya da baya, a hare hare 16 da ya fuskanta, a kasar da akewa kallon mai kwatanta demokradiyya a gabashin Afirka.

Masu lura da lamuran siyasa na cewar, babu 'yancin fadin albarkacin baki, balle walwala a karkashin mulkin Magufuli mai shekaru 60 da haihuwa, da jam'iyyarsa ta Chama Cha Mapinduzi ko kuma CCM da ke mulki tun daga shekara ta 1961.