1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi: Ana gudanar da zaben shugaban kasa cikin fargaba

Abdourahamane Hassane
May 20, 2020

Al'umma a Burundi na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da ake cike da fargaba na samun tashin hankali bayan yakin neman zaman da aka yi cikin tankiya.

https://p.dw.com/p/3cXM9
Burundi Wahlen 20.05.2020
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

Zaben wanda zai kawo karshen mulkin Pierre Nkurunziza, wanda ke kan mulkin tun a shekara ta 2005 wanda kuma ba zai sake tsayawa takara ba. Za a fafata tsakanin Janar Évariste Ndayishimiye na kusa da Nkurunziza, da kuma jagoran 'yan adawar Agathon Rwasa. Ana gudanar da zaben ne dai ba tare da halatar wakilai masu saka ido ba na MDD da kuma na kungiyar tarrayar Afirka ba AU, saboda gwamnatin ta Burundi ta ki ammincewa da su.