Zaben Mali cikin rashin tsaro.
March 29, 2020An dai gudanar da zaben cikin yanayi na fargaba ta la'akari da matsalar tsaro da kuma annobar Coronavirus da ke ci gaba da tafka ta'asa a sassan duniya, ga kuma madugun 'yan adawar kasar Soumaila Cisse da ake kyautata zaton yana hannun 'yan ta'adda da suka addabi kasar, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai wa ayarinsa farmaki kuam har aka kamalla zaben ba a ji duriyarsa ba, lamuran da suka matukar ragewa zaben 'yan majalisun armashi. Sadou Diallo guda ne daga cikin wadanda suka tsaya takara a zaben 'yan majalisun, ya ce an kwashi fiye da shekara guda ana jinkirta shi, wanda kuma ya sabawa dokar kasar don haka ne ya zama wajibi a yi zaben a wannan karon kamar yadda aka tsara.
Coronavirus ba hujjar daga zabe ba ce
Zaben na zuwa ne bayan da a makon jiya, aka sami mutum na farko a kasar Mali da ya kamu da cutar Coronavirus, mai shekaru saba'in a duniya da ya dawo kasar ne daga kasar Faransa, lamarin da yanzu yasa aka killace wasu mutum kimanin ashirin da ake zaton sun yi mu'amala da datijjon. Wnnan dai bai isa hujjar dakatar da zaben ba a ganin wasu 'yan kasar. Ana sa ran hukumar zaben kasar za ta bayyana sakamakon zaben a 'yan kwanaki masu zuwa, yayin da ake sa ran gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar 19 ga watan Afrilu mai zuwa.