1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Kakkabo jirgin Amirka mara matuki

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2019

Dakarun juyin-juya halin Musulunci na kasar Iran sun sanar da cewa sun kakkabo wani jirgin sama mara matuki mallakar kasar Amirka da ke shawagi a sasarin samaniyar kasar.

https://p.dw.com/p/3KlQS
US Drohne MQ-4C Triton
Iran ta kakkabo jirgin saman Amirka mara matuki a sasarin samaniyar kasartaHoto: U.S. Navy/Handout via Reuters

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fuskantar karuwar fargabar barkewar yaki tsakanin Tehran da Washington. Dakarun  juyin-juya halin Musuluncin na Iran din sun nunar da cewa sun kakkabo jirgin saman marar matuki kirar RQ-4 "Global Hawk" mallakar Amirka a gundumar Hormozgan da ke yankin Kudancin kasar. Gundumar ta Hormozgan da ke gabar Tekun Fasha na zaman yankin da ake kyautata zaton ka iya zama filin daga tsakanin kasashen biyu da ba sa ga maciji da juna, in har ba su kai zuciya nesa dangane da batun shirin makamashin nukiliyar Iran din ba.