Farmakin ramuwa kan MTN
February 23, 2017Talla
Kakakin MTN a Najeriya ya fadawa manema labarai cewa, mutanen suna zanga-zanga ne kan hallaka 'yan Najeriya wanda zauna gari banza masu gyamar baki suka yi a Afirka ta Kudu. Farmakin an kai shi ne a ofishin MTN da ke Abuja wanda, shi ne babban cibiyar sayarda layin salau na kamfanin a kasashen Yammacin Afirka da kuma ofishin hulda da jama'a na MNT. A cewar kakakin na MTN, wadanda suka kai farmakin sun lalata na'u'rorin kamfanin, kana suka sace wayoyin salula na kwastomini da ke cikin ofishin a lokacin da masu boren suka shiga.