1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yanayin aiki na zamani: Ba mafita idan ba ilimi

Becker, Andreas AS/MNA
September 21, 2021

Kasuwar kwadago a Jamus na fuskantar manyan sauye-sauye da ba ta shirya tinkararsu ba. Shin sabuwar gwamnatin da za a girka a nan gaba za ta iya tinkarar wannan kalubale da nufin magance shi kuwa?

https://p.dw.com/p/40btf
Roboter-Kellner | Türkei Istanbul
Hoto: Islam Yakut/AA/picture alliance

Yanayi na samar da aiki da ma aiwatar da shi a Jamus na ci gaba da fuskantar manyan sauye-sauye, sai dai ya zuwa yanzu ba wani hobbasa da masu rike da madafun iko ke yi wajen ganin an tinkari wadannnan sauye-sauye musamman ma wadanda zamani ya kawo, batun da masana ke cewa na iya zamewa kasar babban kalubale.

A shekarun da suka gaba musamman ma daga 2005 zuwa yanzu, hukumomi a Jamus sun yi namijin kokari wajen rage yawan marasa aikin yi, hasali ma alkaluman da aka fidda sun nuna cewar yawan marasa aikin yi daga wancan lokacin zuwa yanzu ya ragu da kusan rabi. Duk da cewar an gamu da kalubale na annobar corona a baya-bayan nan, lamura ba su sauya ba domin adadin wanda suka rasa aikinsu bai taka kara ya karya ba.

Sai dai duk da wannan ci-gaban da aka samu, masana na ganin kasar ka iya shiga wani yanayi na rashin aikin yi duba da yadda ake maye gurbin ayyuka masu wahala da na'urori da ake kirkira ko ma na'urar kwamfuta kan iya yin irin wadannan ayyukan.

Tun ba yau ba mutum mutumin kwamfuta suka maye gurbin mutane a masana'antun kera motoci, kamar nan a kamfanin motoci na VW
Tun ba yau ba mutum mutumin kwamfuta suka maye gurbin mutane a masana'antun kera motoci, kamar nan a kamfanin motoci na VWHoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

Iri-iren aiyyukan da za su shiga irin wannan taskun nan gaba su ne ayyuka da jama'a kan samu ba tare da sun yi zurfn karatu kuma tuni ma aka kama wannan hanya inji Hilmar Schneider na wata cibiya da ke bincike kan ayyukan yi a birnin Bonn, a wata zantawa da ya yi da DW.

"Tuni fa muka yi nisa a wannan godabe kuma mun ma rigaya mun kusa kaiwa kololuwa. An dan kwan biyu da karkata akala ta aiki da za a iya da na'urori ko ma injina."

Ma'aikatu da masana'antu da dama da kuma wurare da ke sarar da kayayyaki ga 'yan kasuwa na daga cikin wadanda suka kama wannan hanya ta maye gurbin mutane da na'urori ko kwamfuta wajen aiwatar da wasu daga cikin ayyukansu kamar yadda kwararru suka nuna, kuma a cewarsu nan gaba ma abin zai shafi kamfanoni da ke dakon kaya domin akwai yiwuwar ci-gaban ya sanya jingine direbobin manyan motoci a koma amfani da motocin da ke sarrafa kansu. Haka ma abin yake ga kamfanoni na motocin haya musamman ma na tasi-tasi.

Suma dai masana halayyar dan Adam sun fara nuna fargaba kan wannan sauyi da ci-gaba na zamani ya haifar, sai dai sabanin abin da sauran kwararru ke hasashe na wanda matsalar za ta fi shafa wato wanda ba su yi zurfin karatu ba. 

Injuna cire kudi na bankuna sun zama wurin hada-hadar kudi da sauran ma'amala da banki
Injuna cire kudi na bankuna sun zama wurin hada-hadar kudi da sauran ma'amala da bankiHoto: picture-alliance/dpa

Farfesa Roland Verwiebe na Jami'ar Potsdam da ke gabashin Jamus na ganin kwararru ma za su dandana kudarsu nan gaba.

"Na tabbata muna fuskantar babban sauyi amma sabon abu da za mu gani game da wannan ci-gaba shi ne ma'aikatan da suka yi zurfin karatu ma za su gamu da kalubale, cikinsu kuwa har lauyoyi domin irin bayanai da mutane kan ruga wajensu su nema za a iya samunsu ta hanyar amfani da fasaha ta zamani. Haka ma abin yake ga kwararrun masu fassara ta harsuna."

Baya ga lauyoyi da wannan lamari zai shafa, ma'aikata na bankuna ka iya shiga tasku musamman ma idan aka yi la'akari da yadda bankuna ke rage yawan ma'aikatansu saboda sabbin tsare-tsare da za ka iya aikewa da kudi ko samunsu ko ma bude asusun ajiya ba tare da mutum ya je bankin da yake hulda da shi ba.

Wannan yanayi da aka tsinci kai a cikin dai ya sanya masana yin kira ga hukumomi da su tashi haikan wajen yi wa lamarin dabaibayi tare da neman mafita don ceton ayyukan mutane da kuma gujewa fadawa yanayi na yawaitar marasa aikin yi.