1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata kan ganawar Merkel da Trump

Suleiman Babayo
March 13, 2017

Angela Merkel za ta gana da Shugaba Donald Trump a karo na farko bayan sukar da ya yi wa Jamus kan batutuwa da yawa.

https://p.dw.com/p/2Z6ec
Angela Merkel da Donald Trump
Angela Merkel da Donald TrumpHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler/R. Sachs

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana shirin ganawa a karon farko da Shugaba Donald Trump na kasar Amirka wanda ya dare madafun iko cikin watan Janairun bana. Ganawar tasu na zuwa ne yayin da danganta tsakanin kasashen biyu ta shiga mawuyacin hali sakamakon kalaman Shugaban na Amirka kan batutuwa da dama da suka shafi Tarayyar Turai da kasuwanci. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wadda take neman wa'adin mulki na hudu, ta yi zamani da Shugabannin Amirka biyu da suka shude, wato George W Bush da Barack Obama, amma babu lokaci mai tsauri kamar yanzu da Shugaba Donald Trump ke iko saboda matakan neman kare Amirka bisa cinikayya da sauran wasu batutuwa.

Josef Janning, Shugaban kula da hulda na kasashen ketare a ofishin Tarayyar Turai da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus ya ce lokaci ne mai tsauri:  "Duba da siyasar Amirka, ana ganin abu ne mai sarkakiya da ba a taba gani ba zuwa wannan lokaci."

USA Donald Trump vor dem US-Kongress in Washington
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Lo Scalzo

Shugaba Donald Trump na Amirka na zama babban kalubale da Shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel ta ke fuskanta bisa dangatakar kasashen gabar tekun Atlantika kawo yanzu. Kuma a gida tana fuskanatar wani kalubale daga babbar jam'iyyar adawa ta SDP a zaben da ke tafe. A cewar Farfesa John Harper masanin manufofin kasashen ketere na Amirka na jami'ar Johns Hopkins da ke birnin Bologna na kasar Italiya haka dakile hanzalin 'yan siyasa masu nuna kishin kasa na Tarayyar Turai:

"Abin da nake tsammani daga wannan ziyara shi ne akalla ta shawo kan Trump ya daina caccakar kungiyar Tarayyar Turai, ya kuma daina goyon bayan 'yan siyasa masu ra'ayi irin na Marine Le Pen."

Deutschland Angela Merkel auf der Handwerksmesse in München
Hoto: Reuters/M. Rehle

Baya ga 'yan siyasa na kasashen Turai masu nuna kishin kasa, akwai kuma barazana daga kasar Rasha, inda Shugabar gwamnatin Angela Merkel za ta yi bayanin halin da ake ciki ga Shugaba Donald Trump da matsayin kasashen Turai. Yayin da ake samu bambance-bambance tsakanin bangarorin, Merkel tana neman ganin an mutunta abubuwa da aka tsayar kamar a kungyiar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20, a cewar Josef Janning na ofishin Tarayyar Turai da ke birnin Berlin.

"Daya daga cikin burin da take da shi na zama samun tabbataci daga bakin sabon Shugaban kan shirin kungiyar G20 na kasashe da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki na sake fasalin hadin kai bisa harkokin hada-hada."

Jamus za ta karbi bakuncin taron na G20 a birnin Hamburg lokacin bazara da ke tafe. Kuma a cewar Farfesa John Harper masanin manofpofin kasashen ketere Amirka ganawa tsakanin shugabannin tana da wata fa'ida. Babu dai wata fata bisa yiwuwar samun aiki tare bayan wannan ganawa, yayin da Merkel ke tunanin zabe, Trump a nashi bangaren yana neman nuna abin da ya yi wa Amirkawa ne.