Fatan alherin Angela Merkel a shekara ta 2012
December 31, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi gargadiɗin cewar, za'a fuskanci mawuyacin hali a sabuwar shekarar da ake shirin shiga, musamman ma a ƙasashen dake amfani da takardar kudi na euro. Sai duk da haka za'a kyakkyawar fata dangane da hakan. A jawabinta na sabuwar shekara Merkel tace wannan a shekara mai karewa, shekara ce dake cike da alhini. Duniya ta fuskanci mawuyacin hali na neman sauyi da kuma bala'i daga indallahi.
Ta ce shekarar ta fara ne da guguwar neman sauyi a yankin arewacin Afrika da gabas ta tsakiya, domin samar da tafarkin ingantacciyar demokraɗiyya. A watan Maris kuwa kasar Japan ta fuskanci mawuyacin hali sakamakon tsinkewar Igiyar ruwa na tsunami biyo bayan girgizar ƙasa, wanda suka haifar matsaloli a tashoshin nukiliyar Fukoshima, batu da ya jagoranci Jamus tsara kawar da dukkan tashoshin nukiliyarta nan da shekara ta 2022.
Merkel tace ƙasashen Turai a nasu ɓangaren na fama da matsalar karayar tattalin arziki, wanda har yanzu da yawa daga cikinsu ke kokarin samar da hanyar farfaɗowa, duk da cewar da sauran tafiya.
Kazalika shugabar ta jamus ta kare manufofin da tsaro da nahiyar ta sanya a gaba, waɗanda ke da nufin tabbatar da zaman lafiya, 'yancin walwala, adalci, kare hakkin al'umma da tabbatar da democraɗiyya.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman