1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan Ban Ki-moon kan taron sauyin yanayi

Mouhamadou Awal BalarabeDecember 4, 2014

Babban magatakar Majalisar Dinkin Duniya ya danganta taron kwararru na Lima da zakaran gwajin dafi na taro kan dumamar yanayi na birnin Paris a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/1DzRx
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Elfiqi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya yi fatan ganin a cimma kudirin yarjejeniya kan dumamar yanayi a babban taron kwararru kan muhalli da ke gudana a birnin Lima na kasar Peru. Mista Ban ya yi ma amfani da wannan dama wajen yaba yarjeejiyar da kasashen china da Amirka suka cimma wacce ta tanadi rage gurbatacciyar iska da suke fitarwa a duniya.

Hakazalika babban magatakardar Majalisar ta Dinkin Duniya ya nuna farin cikinsa game da shiga da Jamus ta yi domin a jera da ita a kokarin da ake yi na rage dumamar yanayi a duniya. Ita dai gwamnati ta Jamus ta amince da wani shiri wanda zai bata damar cimma muradin rage adadin iska mai guba kan nan da 2020.

A birnin Paris na Faransa ne za a gudanar da babban taron kan sauyin yanayi a karshen shekara ta 2015. Babban burin da aka sa a gab adai shi ne cimma yarjejniya kan sauyin yanayi, shekaru biyar bayan cin tura da na birnin Copenhagen ya yi.