Fatan warware rikicin gabas ta tsakiya
July 31, 2013Wani Jami'in diplomasiyyar a birnin kudus din kasar Isra'ila ya bayyana cewar, cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu cikin watanni tara, fata ne kawai amma ba wa'adi ba. Babban jami'i a ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus Michael Ratney, ya fada wa taron manema labaru cewar, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai rika ziyartar yankin akai-akai, domin ganin yadda shirin neman zaman lafiyar ke tafiya. Ya kara da cewar wani Janar na Amurka mai ritaya John Allen, zai yi aiki kafada da kafada da bangarorin biyu a kan batutuwan tsaro. A wannan mako ne dai aka kaddamar da sabuwar tattaunawa tsakanin Isra'ila da Palastinu, bayan rushewar da yayi tun shekaru biyar da suka gabata. Kerry ya nunar da cewar, akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu nan da watanni tara masu zuwa.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasir Awal