1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗi tashin harkokin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniDecember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CcKK

Jam´iyyun siyasa a Pakistan sun fara yaƙin neman zaɓe na gama gari, kwana ɗaya bayan ɗage dokar ta ɓaci. Matakin ya kuma haifar da ci gaba da aiki da kundin tsarin mulƙin ƙasar da aka dakatar a baya. Jam´iyyun adawa na ƙasar sun zargi shugaba Musharraf da shirya maguɗi a zaɓen na gama gari. Pakistan dai ta shafe tsawon makonni shida a ƙarƙashin dokar ta ɓacin. Shugaba Musharraf dai a baya ya ce ya kafa dokar ta ɓacin ne a sabili da taɓarɓarewar harkokin tsaro a ƙasar. Shugaban na Pakistan ya kuma tabbatar da cewa komai zai tafi dai-dai dangane da wannan zaɓe.

Kafafen yaɗa labarai sun rawaito tsohuwar Faraministar ƙasar, Benazir Bhutto na yaba matakin ɗage dokar ta ɓacin, to amma kuma har yanzu a cewarta akwai sauran rina a kaba.