1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗi tashin harkokin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniDecember 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiJF

Jam´iyyar Benazir Bhutto ta amince da naɗin ɗanta da kuma mijinta, a matsayin waɗanda zasu jagoranci Jam´iyyar. Bilawal Zardari ɗan shekaru 19, a yanzu haka shi ne shugaban jam´iyyar ta PPP. Shi kuma Asif Ali Zardari, a matsayin mataimakinsa. Rahotanni sun ce Mr Asif zai ci gaba da lura da harkokin Jam´iyyar, har lokacin da Zardari zai kammala karatunsa. Tuni dai Jami´an tsaro na ƙasar su ka ƙaddamar da binciken waɗanda keda hannu, a kisan gillar da akayiwa Benazir Bhutton. A waje ɗaya kuma hukumar zaɓe ta ƙasar na shirin gudanar da taro a yau. Taron zai duba yiwuwa ko kuma akasin haka na gudanar da zaɓen gama gari a ƙasar ne. A baya dai Pakistan ta shirya yin zaɓen ne, a ranar 8 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2008.