Ficewar Girka daga EU ba ta taso ba
February 20, 2015A ranar Juma'a ne Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters yana da kyakkyawan yakini cewa gwamnatinsa za ta cimma muradin da ta ke da shi na ganin an tsawaita wa'adin da kasashen da ke binta bashi ya zuwa watanni shida nan gaba, adaidai lokacin da mahukuntan birnin Berlin na Jamus ke nuna adawa da wannan kari.
A cewar shugabar gwamnatin Jamus akwai bukatar warware wasu tambayoyi da suke bukatar amsoshi a kan basukan da aka ba wa kasar ta Girka:
"Domin kara wa'adin lokaci ga kasar ta Girka ta biya basukan da ake bin ta muna son ganin sauyi na ci gaba ta yadda za mu sami abin gaya wa sauran kasashe na Turai , akwai tambayoyi cike da murdiya da ba a bada amsarsu ba, dole a cimma wata matsaya, ba zan bayyana komai ba yanzu ministocin kudinmu zasu yi muhawara a kan wannan batu sosai"
Bayan tattaunawar ta birnin Paris shugaba Markel da Francois Holland sun bayyana cewa kasar ta Girka dole ta ci gaba da zama cikin kungiyar kasashen da ke amfani da kudin Euro batun fice