Ficewar kasashen Afirka a kotun ICC
November 4, 2016A sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka za mu fara ne da jaridar die Taz, wace ta ce Najeriya ta jaddada ci gaba da zama mamba a kotun hukunta manyan laifuka na duniya. Jaridar ta ce sabanin abokiyar goggaya da Najeriya a nahiyar Afirka, wato kasar Afirka ta Kudu, wace ta sanar da ficewa daga kotun ICC, amma an jiyo mai wakiltan Najeriya a MDD na cewa, su kam ba abinda zai fidda su karkashin kotun. A wani zaman kwamitin sulhu na MDD ya yi, Najeriya ta jadda matsayin ta, na ci gaba da yin biyayya ga yarjejeniyar kotun hukunta manyan laifuka. A kwanannan dai kasashen Burundi, Afrika ta Kudu da Gambiya sun sanar da ficewa daga kotun ICC, inda suke zargin kotun da hukunta 'yan Afirka kawai, yayinda da yake barin turawa da ke aikata laifi.
Sai jaridar Neue Zürscher Zeitung, inda jaridar ta yi tsokaci bisa koran kwamandan dakarun MDD a Sudan ta Kudu. A cewar jaridar an samu sojojin MDD da laifin kin kawo dauke a lokacin da sojojin Sudan ta Kudu ke cin zarafin jama'a yayin wani gumurzu tsakanin sojan na gwamnati da 'yan tawaye a ranar 11 ga watan Julin bana. Jaridar ta kara da cewa a wannan ranar cikin wani otel da ke Juba babban birnin kasar, an ci zarafin mata da sauran ma'aikatan otel, kana kuma aka lakada wa wani dan jaridan Sudan ta Kudu duka. A lokacin sojojin MDD da ke aiki a kusa da wajen, sun ki amsa wayoyin neman dauki da aka yi ta buga musu. Hasalima sojojin na MDD sun yi ta fadawa masu neman daukin cewa basu da lokaci, domin suna bakin aiki. bisa wadannan aikata laifin yasa sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya dau matakin dakatar da kwamandan na sojojin kiyaye zaman lafiya.
Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi labarinta ne kan dakarun kiyaye zaman lafiya. inda tace bisa ga dukkan alamu sojojin Jamus da ke aiki a kasar Mali za a kara wa'adin aikinsu. Jaridar ta ce an tsara tsawaita wa'adin aikin sojojin Jamus ne, domin su samu damar yin jigilar kayakin yaki da suka hada da manyan motoci daga birnin Goa da sauran sassan arewacin kasar ta Mali.
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland cewa ta yi. Batun lalata da mata ya zama ruwan dare a kasar Kamaru. A Kasar Kamaru kamar sauran kasashen Afirka da yawa, batun lalata da mata wani abu ne da dangi basu cika bayyanawa a fili ba, don haka ko da an yi mata ciki akan yi watsi da su, kusan babu wanda ke bin kadu don ganin an zakula wanda ya yi wa matar ciki. Jaridar ta ce, bisa wannan matsaloli na gyama da tsangwama, yanzu a kasar Kamaru wasu matasa sun bullo da wata manhajar zamani da za ta rika ilmantar da mata kan yanayin daukar ciki. Ana bada bayanai ta wannan manhajar ba tare da fadan sunan matar ba. Inda ake sakaye sunayen don kare matan.