FIFA: Kariya ga 'yan wasa a Internet
November 17, 2022Talla
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta kaddamar da sabuwar manhaja da za ta bi diddigin kalaman batanci da cin tarafi a yanar gizo a lokacin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Qatar.
Wannan sabon tsari zai bada kariya ga yan kwallo fiye da 830 daga cin zarafi a shafukan sada zumunta a lokacin wasannin.
David Aganzo shugaban kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa na duniya ya ce matakin zai taimaka wajen kare yan wasan daga illar da irin wannan cin zarafi zai haifar gay an wasa musamman ga lafiyarsu ko kuma yanayin walwalarsu.