1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FIFA: Kasashe uku za su dauki nauyin gasar 2030

Abdullahi Tanko Bala
October 5, 2023

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce Morocco da Portugal da Spain za su dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2030 sai dai wasu wasannin za a yi su ne a Uruguay da Argentina da Paraguay

https://p.dw.com/p/4X7VD
Kofin duniya na 2030
Kofin duniya na 2030Hoto: Mike Egerton/PA Wire/emipics/picture-alliance

Hukumar ta FIFA a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce wasannin da za a yi a kudancin Amurka na daga cikin tsare tsaren bukukuwan cika shekaru 100 da fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka yi a Uruguay a cewar shugaban hukumar kwallon kafa ta kudancin Amurka Alejandro Dominiguez

Hadin gwiwar daukar nauyin gasar kwallon kafar ta duniya har yanzu yana bukatar amincewa a hukumance a shekara mai zuwa a taron kasashe 211 da ke cikin FIFA.

Kungiyoyi 48 da za su buga wasanni 104 za su fara karawa ne a tsakanin watan Yuni zuwa Yuli na 2030 a Uruguay da Argentina da Paraguay kafin danganawa zuwa kasashen Spain da Portugal da kuma Morocco masu naukar nauyin gasar.