Kasar Finland ta zama memba a NATO
April 4, 2023Shigar Finland cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO na zama wani sabon babi tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar Ukraine.
Za a gudanar da biki na musanman a yau Talata hudu ga watan Aprilu da ke zama ranar zagowar cika shekaru 74 da yankewa kasar ta Finland da ke Arewancin Turai cibiya wacce kuma ke raba iyaka ta sama da kilomita 1.300 da kasar Rasha.
Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewa shigar Finlande cikin kungiyar kawancen tsaron zai kara wa NATO karfi ta ko wacce fuska. Sannan a daya gefe kuma Stoltenberg ya ce yana da yekinin cewa nan zuwa gaba kasar Ukraine ma za ta cika burinta na zama memba a kungiyar amma yanzu ba maganar wannan ne a gaba ba, suna son su ga Ukraine din ta sake dinkewa ta zama kasa daya mai cin gishin kanta.