Boris Johnson ya killace kanshi
November 16, 2020Talla
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan Brexit inda Birtaniya ta ce tana kan bakarta tare da fatan cimma yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar Tarayyar Turai.
Yayin zaman kilace kai, Firaminista Johnson daga gidansa zai ci gaba da amfani da kafar sadarwa ta bidiyo wato Zoom da wasu kafofi yayin da ake gabar karshe ta tattaunawar Brexit a birnin Brussels.
In dai ba a manta ba a watan Afrilun da ya gabata ne dai Boris Johson ya shiga halin rai kwakwai mutu kwakwai sanadiyyar kamuwa da cutar corona.