Firaministan Birtaniya yana ziyara a Jamus
April 24, 2024A wannan Laraba Firamnista Rishi Sunak na Birtaniya ke kawo ziyara ta farko zuwa birnin Berlin na Jamus tun lokacin da ya dauki madafun iko watanni 18 da suka gabata. Yayin zirayar Firaminista Sunak zai gana da Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz inda za su mayar da hankali kan hanyoyin taimakon Ukraine kare kanta da kuma yakin da ke faruwa a yankin Zirin Gaza na Falasdinu tsakanin kungiyar 'yan ta'adda ta Hamas da isra'ila.
Shekaru hudu da suka gabata Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar Tarayyar Turai, amma ta ci gaba da kasance kawar Jamus ta kut-da-kut inda duk kasashe suke kungiyar tsaron NATO, da kungiyar G7 ta gaggan kasashe masu karfin arzikin masana'antu da kuma kungiyar G20 ta kasashen da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya.
Wannan ziyara ta firaministan Birtaniya tana zuwa kwana guda bayan majalisar dokokin kasarsa ta amince da wani shiri mai cike da cece-kuce na tisa 'yan gudun hijira da suka shiga kasar ta Birataniya ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Ruwanda da ke yankin nahiyar Afirka.