Sabuwar wasikar Girka ga hukumomin EU a Brussels
July 1, 2015Firaministan Girka Alexis Tsipras ya dauki sabon mataki a kan rikicin bashin kasarsa. A cikin wata wasika da ya aike wa hukumomin tarayyar Turai a birnin Brussels, Tsipras ya ce zai amince da sabbin jerin shawarwari da amsu bin kasarsa bashi za su bayar. Rahotanni daga majiyoyin EU sun ce ministocin kudi na kasashe masu amfani da kudin Euro za su tattauna kan wasika a wani taro ta kafar wayar tarho da za su yi in an jima a wannan Laraba.
Sai dai a martanin farko da ya mayar ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble ya ce sabuwar wasikar ba ta kunshi wani bayani mai gamsarwa ba.
"Mun ce har yanzu kofa a bude take. A shirye muke mu tattauna a kowane lokace idan suna son mu tattauna za mu yi hakan. Mun samu labarin cewa za a rubuta wata wasika ta biyu, wadda yanzu haka kuma ta iso gare mu, amma ba ta ba da wani karin bayani ba."
Da yammacin ranar Talata wa'adin shirin tallafawa Girka ya kare.