Firaministan Girka ya yi murabus
August 21, 2015Firaministan Alexis Tsipras na kasar Girka ya yi murabus tare da kira da a sake gudanar da zaben kasa baki daya. Ana dai yi wa matakin da Tsipras ya dauka na yin murabus kallon kokarin gujewa tawayen da yake ci gaba da fuskanta daga jam'iyyarsa ta Syriza sakamakon amincewa da matakan ceto tattalin arzikin kasar da ya yi, inda da dama daga cikin 'yan majalisun dokokin kasar na jam'iyyar ke ganin cewa Tsipras ya ba su kunya ta hanyar bayar da kai bori ya hau ga masu bayar da bashin.
A hannu guda kuma murabus din na Tsipras na zamowa wani mataki na tabbatar da goyon bayansa ga kasashe masu bayar da bashi da za su tallafawa Girkan a karo na uku. Tuni dai ministocin kudi na kasashen da ke cikin kungiyar kasashe masu amfani da kudin Euro wato Eurozone suka amince da matakin farko na ceto Girka karo na uku cikin wannan mako.