Firaministan Haiti ya yi murabus daga mukaminsa
March 12, 2024Zanga-zanga babu kakkautawa ce dai ta jijjiga kasar ta Haiti a 'yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya rikide ya haddasa tashin-tashinan da a yanzu firaminista Ariel Henry ya gwammace hakura da kujerarsa domin kwantar da tarzomar da ke ruruwa a cikin hanzari. Kamar yadd Mr. Henry ke cewa
"Bayan da majalisar ministoci na ta amince shugaban kasa ya kafa wata majalisa ta rikon kwarya, mun amince za a sake zakulo wasu mutane don nada su cikin majalisar ministocin don kasarmu ta matsa zuwa mataki na gaba. Idan har aka yi hakan, gwamnatin da nake jagoranta za ta yi gaggawar tafiya.''
Kafin cimma wannan matsaya dai sai da aka kai ruwana rana. Shugabannin kungiyar kasashen Caribbean da ake wa lakabi da CARICOM sune suka kira taro na gaggawa kan dambarawar ta kasar Haiti a kasar Jamaica a Litinin din da ta gabata, inda a karshen taron wanda sakataren kula da harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya halarta, firaminista Henry ya amince ya yada kwallon mangwaro don ya huta da kuda kamar yadda Irfaan Ali, shugaban kasar Guyana daya daga cikin kasashen da ke kungiyar ta Caribbean ya yi karin haske.
"Muna farin cikin sanar da yarjejeniyar shirin gwamnatin rikon kwarya wacce za ta ba da damar mika mulki cikin ruwan sanyi domin ci-gaba da ayyukan shugabanci da zai samar da tsaro ya kuma share fagen shirya sahihin zabe, mun gamsu da cewa hakan zai sanya a dawo da doka da oda a Haiti.''
Tun daga shekara ta 2021 Henry ke rike da mukamin da aka nada shi ba tare da gudanar da zabe ba bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Haitin da ya gabata, lamarin da ya kara dagula siyasar kasar mai tafiya da 'yan daba. Garkuwa da mutane irin na arewacin Najeriya da sauran muggan laifuka sune ke kara karuwa kusan kullum a Haiti lamarin da ya sanya kasar Kenya daga kasashen Afirka bugar kirjin bayar da gudunmuwar dakarunta domin aikin dawo da doka da oda a Haitin a karkashin wata runduna ta Majalisar Dinkin Duniya. Byron Adera, tsohon shugaban rundunar tsaron Kenya ta musamman ya fadi alfanun hakan ga Kenya.
"Idan muka yi aiki tukuru a ketare za mu samar wa kanmu mutuncin da za mu iya tutiya da shi har ma mu bugi kirjin cewa za a yi wa Kenya kallon kasa mai karfin gaske a idon duniya.''
Haiti dai na cikin kasashen yankin Caribbean da suka yi kaurin suna wajen ayyukan 'yan daba, inda a galibi zanga-zangar lumana domin nuna fushi kan rikide zuwa tashin hankali ta hanyar tsallake tanadin da dokoki suka yi wajen nuna fusata.