1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Iceland ya ajiye aiki

Suleiman BabayoApril 5, 2016

Firaministan kasar Iceland ya yi murabus sakamakon bankado abun kunya na kauce biyan kudaden haraji.

https://p.dw.com/p/1IPro
Sigmundur David Gunnlaugsson Island Premierminister
Hoto: picture-alliance/dpa/Str

Firaminista Sigmundur David Gunnlaugsson na kasar Iceland ya ajiye aiki, kwana guda bayan gangamin neman ya sauka daga madafun iko bayan bankado cewa yana cikin wadanda suke amfani da kamfanoni na kasashen ketere domin kauce biyan kudaden haraji.

Mataimakin shugaban jam'iyya mai mulki Sigurdur Ingi Johannsson kana ministan kula da kamun kifi da aikin gona ya tabbatar da haka a wannan Talata. Shi dai Firaminista Sigmundur David Gunnlaugsson ya jafar da kwallon mangoro domin ya huta da kuda, inda ya zama mutum na farko da bankado abin kunya na kamfanonin boye kudade domin kauce biyan haraji ya ritsa da gwamnatinsa.