Firaministan Pakistan zai bayana gaban kotun tsarin mulkin ƙasa bisa zargin cin hanci
January 16, 2012Baya ga taƙaddama da sojoji, gwamnatin farar hular Pakistan ta doshi hanyar yin mummunan fito na fito da hukumomin shari'ar ƙasar. A dangane da badaƙalar cin hanci da rashawa da ya shafi shugaban ƙasa Asif Ali Zardari, kotun kare kundin tsarin mulkin ƙasa ta gayyaci firaminista Yousouf Raza Gilani da bayyana gabanta a ranar Alhamis. Shi dai Gilani na fsukantar barazanar hukunci bisa laifin raina kotun ƙolin Pakistan. Duk da umarnin alkalai, firaministan na ƙoƙarin yin rufa-rufa akan zargin da ake wa shugaba Zardari na halasta kuɗin haramun a shekarun 1990, inda ya yi nuni da rigar kariya da shugaban ke da ita. A baya bayan nan alƙalan kotun kare kundin tsarin mulki sun yi barazanar tsige firaminista Gilani idan ya ci-gaba da ƙin bin umarnin kotu. Sai dai masu sukar lamiri na zargin alƙalan da haɗa baki da sojoji domin kifar da gwamnatin farar hula.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi