Firamnistan kasar Girka ya kira zaben gaggawa
December 29, 2014Talla
A wannan Litinin Firamnistan kasar Girka Antonis Samaras ya bayyana kiran zaben gaggawa kafin lokaci da za a gudanar ranar 25 ga watan gobe na Janairu, wanda ake zaton zai kawo masu nuna kiyayya ga matakan tsuke bakin aljihu zuwa kan madafun iko.
Kiran zaben ya zama wajibi bayan da dan takaran shugaban kasa da gwamnati take mara masa baya Stavros Dimas ya samu kuri' 168 daga cikin 180 da yake bukata domin zama shugaban kasa, abin da ya sa tilas a rusa majalisar dokokin nan da kwanaki 10 masu zuwa. Kiran zaben zai shafi tattalin arzikin kasar wanda tun shekara ta 2012 ya fada gadari.
Watanni shida da suka gabata tattalin arzikin kasar ta Girka ya fara farfadowa.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu